Mathieu zai yi jinyar makonni uku

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An bai wa Mathieu jan kati a karawar da suka yi da Manchester City

Mai tsaron baya na Barcelona, Jeremy Mathieu, zai yi jinyar makonni uku.

Dan wasan ya yi rauni ne a ranar Talata a fafatawar da Barcelona ta ci Espanyol daya mai ban haushi a Super Cup na Catalan.

Sauran 'yan wasan Barcelona da suke yin jinya sun hada da Gerard Pique da Jordi Alba.

Shi ma kyaftin din kungiyar, Andres Iniesta, wanda ya yi rauni a gwiwarsa a karawar da Barcelona ta ci Valencia 3-2, zai yi jinyar makonni shida zuwa takwas.

Mathieu ba zai buga wa Barcelona gasar La Liga da za ta yi da Granada da Sevilla ba, da kuma fafatawar da za ta yi da Manchester City a gasar cin kofin zakarun Turai.