Man United ta fitar da Man City a League Cup

League Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wannan ne karo na hudu da Mourinho ya ci Guardiola a haduwa 18 da suka yi

Manchester United ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar League Cup, bayan da ta ci Manchester City daya mai ban haushi.

United ta ci kwallon ne ta hannun Juan Mata, bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Nasarar da United ta yi, ita ce ta biyu a wasanni biyar, kuma karo na hudu da Mourinho ya doke Guardiola a haduwa 18 da suka yi.

Tun kafin karawar, City ta ci United 2-1 a gasar Premier ta bana da suka kara a Old Trafford.

A ranar Asabar ne Chelsea ta ci Manchester United 4-0 a gasar Premier da suka fafata a Stamford Bridge.

West Ham ma ta kai wasan zagaye na gaba bayan da ta doke Chelsea da ci 2-1, Southampton kuwa 1-0 ta ci Sunderland.