League Cup: Arsenal za ta fafata da Southampton

League Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Za a fara wasannin ne a ranar 29 da 30 ga watan Nuwamba

Southampton za ta ziyarci Arsenal a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar League Cup bayan da aka raba jadawali a ranar Laraba.

Arsernal ta kai wannan matakin ne bayan da ta ci Reading 2-0 a ranar Talata, ita kuwa Southampton doke Sunderland ta yi 1-0 a ranar ta Laraba.

Sauran wasannin da za a yi Liverpool za ta karbi bakuncin Leeds, sai Newcastle United ta ziyarci Hull City.

Ita kuwa Manchester United wadda ta fitar da Manchester City daga gasar za ta karbi bakuncin West Ham a Old Traford.

Za a yi wasannin ne a ranar 29 da kuma 30 ga watan Nuwamba.