Vazquez ya tsawaita zamansa a Real Madrid

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Vazquez ya ci wa Real Madrid kwallaye hudu

Lucas Vazquez ya sabunta kwantiragin ci gaba da murza-leda a Real Madrid zuwa Yunin 2021.

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Spaniya, ya koma Madrid a shekarar 2007, yana da shekara 16, inda ya fara wasa a karamar kungiyar.

Ya kuma fara buga wa babbar kungiyar wasa a ranar 12 ga watan Satumba 2015, a karawar da Madrid ta ci Espanyol 6-0.

Vazquez wanda ya yi wa Madrid wasanni 33, ya ci kwallo hudu, ya kuma buga wa tawagar Spaniya wasanni uku.