An yi yamutsi a wasan West Ham da Chelsea

League Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

West Ham ce ta kai wasan daf da na kusa da na karshe

An yi yamutsi tsakanin magoya bayan West Ham da na Chelsea, bayan da suka tashi a wasan League Cup a ranar Laraba.

West Ham ce ta doke Chelsea da ci 2-1, wanda hakan ya sa za ta kara da Manchester United a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar.

Magoya bayan kungiyoyin biyu sun yi ta jifan junansu da robobin ruwan sha da kwandaloli, hakan ya sa jami'an tsaro suka kama mutane bakwai.

Ana ta samun hatsaniya tsakanin magoya baya tun komawar West Ham United sabon filin wasanta.

West Ham ta ce za ta hana duk wanda ta samu da laifi shiga kallon wasa a filin har abada, za kuma ta yi amfani da na'urar daukar hoton bidiyo domin gano masu laifi.