Ronaldo yana kamfar cin kwallaye

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid za ta ziyarci Deportivo Alaves a ranar Asabar

A ranar Asabar za a ci gaba da buga gasar La Liga wasannin mako na 10. Sai dai Cristiano Ronaldo na fama da rashin cin kwallaye a gasar bana.

Dan wasan ya gamu da koma-baya ta fuskar cin kwallaye tun lokacin da ya koma Madrid a shekarar 2009, wanda ya ci guda hudu a bana biyu a gasar La Liga

A tawagar kwallon kafa ta Portugal kuwa, kwallaye biyar Ronaldo ya ci, hudu a karawa da Andorra da daya a fafatawar da suka yi da tsibirin Faroe a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya.

A kakar wasannin bara da aka kammala Luis Suarez ne ya lashe kyautar wanda ya fi yawan cin kwallye a gasar La Liga, inda ya ci 40; guda 30 Ronaldo ya ci a matsayi na biyu.

A kakar wasannin kwallon kafa ta bana Messi na Barcelona ya zura kwallaye 14 a raga a wasanni 11 da ya yi.