Barcelona ta yi karar shugaban La Liga

La Liga

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Messi ne ya ci kwallo na uku inda ya bai wa Barcelona damar samun maki uku a karawar

Barcelona ta yi karar shugaban gudanar da gasar La Liga, Javier Tebas, gaban babbar kotun wasanni ta Spaniya, bayan da ya tuhumi 'yan wasanta a karawar da suka yi da Valencia.

Tebas ya ce Barcelona na da laifin tada yamutsi a karawar da ta ci Valencia 3-2 a wasan da suka yi a ranar Asabar, ta wajen yadda suka dunga yin murnar kwallo na uku da suka ci.

Hukumar ta La Liga ta ci tarar Valencia fam 1,340, bayan da magoya bayanta suka dunga jifan 'yan wasan Barcelona da robar ruwan sha.

Shi ma kwamitin da'a na hukumar ya soki rawar da Barcelona ta taka a wajen yin murnar cin kwallon, inda ya kara da cewar hakan ne ya harzuka magoya bayan Valencia.

Barcelona ta ce wadannan kalaman ba su dace ba.