Arsenal ta lallasa Sunderland da ci 4-1

Alexis Sanchez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alexis Sanchez

A ci gaba da gasar Premier ta Ingila, kulob din Arsenal ya lallasa Sunderland da ci 4-1 a karawar da suka yi ranar Asabar.

Alexis Sanchez da Olivier Giroud ne su ka ci wa Arsenal kwallaye biyu-biyu.

Yanzu Arsenal din na da 23, kuma hakan ya ba kulob din damar komawa saman teburin Premier.

Sai dai ci gaba da kasancewar kulob din a saman teburin ya danganta ne da yadda ta kaya a wasannin da Manchester City da kuma Liverpool za su yi a ranar Asabar din.