Arsenal ta doke Sunderland 4-1

Premier

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sanchez ya ci kwallaye takwas a wasannin bana

Sunderland ta yi rashin nasara a gida a hannun Arsenal da ci 4-1 a gasar Premier wasan mako na 10 da suka fafata a ranar Asabar.

Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Alexis Sanchez a minti na 19 da fara tamaula, bayan da aka dawo ne daga hutu Sunderland ta farke ta hannun Jermain Defoe.

Arsenal ta kara cin kwallaye ta hannun Olivier Giroud a minti na 71 da kuma 76, sannan Alexis Sanchez ya ci ta hudu kuma ta biyu da ya ci a wasan.

Arsenal ta hada maki 23 a wasanni 10 da ta yi a gasar Premier ta bana.