Man City ta dare kan teburin Premier

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City tana mataki na daya a kan teburin Premier

Manchester City ta hau kan teburin Premier, bayan da ta ci West Brom 4-0 a wasan mako na 10 da suka fafata a ranar Asabar.

Sergio Aguero ne ya ci wa City kwallaye biyu kafin a je hutun rabin lokaci a karawar da suka yi a filin wasan West Brom.

Bayan da aka dawo ne daga hutu shi ma Ilkay Gundogan ya zura guda biyu a raga.

Da wannan sakamakon City ta koma ta daya a kan teburin Premier da maki 23 a wasanni 10 da ta yi a gasar.