Liverpool ta samu maki uku a kan Crystal Palace

Asalin hoton, Rex Features
Liverpool tana mataki na uku a kan teburi da maki 23 iri daya da na City da Arsenal
Crystal Palace ta yi rashin nasara a gida a hannun Liverpool da ci 4-2 a gasar Premier wasan mako na 10 da suka kara a ranar Asabar.
Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun Emre Can minti 16 da fara wasa, minti biyu tsakani Crystal Palace ta farke ta hannun James McArthur.
Kafin a je hutu Liverpool ta kara ta biyu ta hannun Dejan Lovren, Crystal Palace ta sake farkewa ta hannun James McArthur.
Liverpool ta ci kwallo na uku daf da za a tafi hutun rabin lokaci ta hannun Joel Matip, kuma saura minti 18 a tashi daga wasan Roberto Firmino ya ci na hudu.
Da wannan sakamakon Liverpool ta hada maki 23 a wasanni 10 da ta buga a gasar ta Premier.