Bale ya tsawaita zamansa a Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Bale ya yi wa Madrid wasanni 11 ya kuma ci kwallaye hudu a bana
Gareth Bale ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da murza-leda a Real Madrid har zuwa shekarar 2022.
Bale mai shekara 27, ya koma Madrid da taka leda daga Tottenham kan kwantiragin shekara shida a shekarar 2013 kan kudi fam miliyan 85, a matsayin wanda aka saya mafi tsada a tarihin tamaula.
A cikin watan Oktoba su ma abokan taka-ledar Bale a Real Madrid Luka Modric da Toni Kross suka tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a kungiyar.
Real Madrid ta sanar da cewar a ranar Litinin, Bale, zai tattauna da 'yan jarida kan batun yarjejeniyar da suka sake kullawa.