An yi kunnen doki tsakanin Kudu da Arewa a dambe

Dambe
Bayanan hoto,

A turmin farko Autan Faya ya buge Shagon Dogon Dan Jamilu

Kimanin wasannin takwas aka dambata da safiyar Lahadi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria, sai dai karawa biyu ce aka yi kisa.

Bangaren Kudawa ne suka fara yin nasara, inda a turmin farko Autan Faya daga Kudu ya buge Shagon Dogon Dan Jamilu daga Arewa.

Ana gama zagayawa da Autan Faya ne sai Arewa suka dauki fansa, inda Shagon Buzu daga Arewa ya buge Shagon Shagon Babangida daga Kudu a turmin farko.

Ga jerin wasannin da aka yi babu kisa:

  • Shagon Shagon Dan Kanawa daga Kudu da Lawwalin Gusau daga Arewa
  • Shagon Bahagon 'Yan Sanda daga Arewa da Ali Shagon Bata isarka daga Kudu
  • Shagon Mahaukaci Teacher daga Arewa da Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu
  • Bahagon Dan Kanawa daga Kudu da Nuran Dogon Sani daga Arewa
  • Autan Fafa daga Arewa da Bahagon Sisko daga Kudu
  • Dogon Na Gobira daga Arewa da Bahagon Dan Kanawa daga Kudu.