Cibulkova ta lashe gasar tennis ta Singapore

Tennis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Cibulkova ita ce ke matsayi na takwas a jerin wadanda suka fi iya kwallon tennis a duniya

Dominika Cibulkova ce ta lashe gasar kwallon tennis ta kwararru ta mata da aka kammala a Singapoe a ranar Lahadi.

Cibulkova 'yar kasar Slovakia, ta lashe kofin ne, bayan da ta doke wadda take a matsayi na daya a jerin iya wasan a duniya Angelique Kerber da ci 6-3 da 6-4.

'Yar wasan mai shekara 27, ta ce rana irin ta Lahadi ba za ta taba mancewa da nasarar da ta yi ba.

Cibulkova ta kai wasan karshe ne a ranar Asabar, bayan da ta ci Svetlana Kuznetsova a dukkan fafatawa ukun da suka yi.