Super Eagles ta gayyaci 'yan wasa 24

Wold Cup Qualifeir
Bayanan hoto,

Nigeria za ta kara da Algeria a Uyo ranar 12 ga watan Nuwamba

Kociyan tawagar kwallon kafa ta Nigeria, Gernot Rohr, ya gayyaci 'yan wasa 24 da za su kara da Algeria a wasan nema shiga gasar kofin duniya a Uyo.

Cikin 'yan wasan da ya bai wa goron gayyata, uku daga cikinsu masu tsaron raga ne, sai masu tsaran baya tara da 'yan wasan tsakiya biyar da kuma masu cin kwallaye su bakwai.

Mai tsaron raga Ikechukwu Ezenwa na IfeanyiUbah, shi ne dan kwallon da yake taka-leda a gasar Firimiyar Nigeria wadda aka kammala.

Nigeria wadda ta lashe kofin Afirka sau uku tana mataki na daya a kan teburin rukuni na biyu, bayan da ta ci Zambia 2-1 a wasan farko da suka yi.

Ga jerin 'yan wasan da aka gayyata Super Eagles:

Masu tsaron raga: Carl Ikeme (Wolverhampton Wanderers, England); Ikechukwu Ezenwa (FC IfeanyiUbah); Dele Alampasu (FC Cesarense, Portugal)

Masu tsaron baya: Leon Balogun (FSV Mainz 05, Germany); William Troost-Ekong (Haugesund FC, Norway); Kenneth Omeruo (Alanyaspor FC, Turkey); Uche Henry Agbo (Granada FC, Spain); Tyronne Ebuehi (ADO Den Haag, The Netherlands); Abdullahi Shehu (Anorthosis Famagusta, Cyprus); Musa Muhammed (Istanbul Basaksehir, Turkey); Elderson Echiejile (Standard Liege, Belgium), Kingsley Madu (SV Zulte Waregem, Belgium)

Masu wasan tsakiya: John Mikel Obi (Chelsea FC, England); Ogenyi Onazi (Trabzonspor FC, Turkey); Wilfred Ndidi (KRC Genk, Belgium); Oghenekaro Etebo (CD Feirense, Portugal); John Ogu (Hapoel Be'er Sheva, Israel)

Masu cin kwallaye: Ahmed Musa (Leicester City, England); Kelechi Iheanacho (Manchester City, England); Moses Simon (KAA Gent, Belgium); Victor Moses (Chelsea FC, England); Odion Ighalo (Watford FC, England); Brown Ideye (Olympiacos FC, Greece); Alex Iwobi (Arsenal FC, England)