Baba Ganaru ya zama kociyan Wikki Tourists

Wikki Tourist

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Kociyan zai jagoranci Wikki ta buga gasar cin kofin Zakarun Afirka ta Confederation

Wikki Tourists ta garin Bauchin Nigeria ta nada Baba Ganaru a matsayin sabon kociyanta.

Kungiyar wadda ta kare a mataki na uku a gasar Firimiyar Nigeria da aka kammala, ta saka hannu a kan yarjejeniya aiki da kociyan na tsawon shekara daya.

Wikki wadda za ta wakilci Nigeria a gasar Zakarun Afirka ta Confederation ta rasa mai horar da 'yan wasanta Abdu Mai Kaba wanda ya koma Akwa United.

Baba Ganaru tsohon kociyan Nasarawa United ya bar aikin jan ragamar Kano Pillars a karshen gasar Firimiyar Nigeria da aka yi, bayan da kungiyar ta kare a mataki na bakwai a gasar.