Chelsea ta doke Southampton da ci 2-0

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Diego Costa ya ci kwallaye takwas a gasar Premier ta bana

Southampton ta yi rashin nasara a gida a hannun Chelsea da ci 2-0 a gasar Premier da suka fafata a ranar Lahadi a filin wasa na St Mary.

Chelsea ta fara cin kwallo ta hannun Eden Hazard a minti na shida da fara wasan, sannan ta ci ta biyu minti 10 da dawowa daga hutu ta hannun Diego Costa.

Da wannan sakamakon Chelsea ta koma mataki na hudu a kan teburin Premier da maki 22, yayin da Southampton tana matsayi na 10 da maki 12.

Chelsea za ta karbi bakuncin Everton a wasannin mako na 11 a gasar ta Premier a ranar Asabar, inda Southampton za ta ziyarci Hull City a ranar Lahadi.