Pepe na Real Madrid zai yi jinya

La Liga

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Pepe ba zai buga wa Portugal wasan shiga gasar cin kofin duniya da za ta yi da Latvia

Mai tsaron baya na Real Madri, Pepe, zai yi jinyar makonni, wanda hakan zai sa ba zai buga karawar da kungiyar za ta yi da Atletico Madrid da Barcelona ba.

Pepe mai shekara 33, dan kwallon tawagar Portugal, ya yi rauni ne a wasan da Madrid ta ci Alaves 4-1 tun kafin a je hutun rabin lokaci a ranar Asabar.

Shi ma dan wasan Real Madrid mai tsaron baya, Sergio Ramos, na yin jinyar ciwon baya da yake fama da shi.

Wasu daga cikin jaridun Turai sun wallafa cewar Pepe zai yi jinyar makonni hudu zuwa shida.

Madrid za ta kara da Atletico Madrid a gasar La Liga a ranar 19 ga watan Nuwamba, sannan ta fafata da Barcelona a farkon makon Disamba.