Manchester City za ta karbi bakuncin Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ce ta daya a kan teburin rukuni na uku
Manchester City za ta karbi bakuncin Barcelona a gasar cin Kofin Zakarun Turai wasa na biyu da za su fafata a Ettihad a ranar Talata.
A wasan farko da suka yi a Camp Nou, Barcelona ce ta shararawa City kwallaye 4-0, kuma Messi ne ya ci uku a karawar, Neymar ya ci guda daya.
Barcelona ce ke mataki na daya a kan teburin rukuni na uku da maki tara, sai Man City ta biyu da maki hudu, sannan Borussia Monchengladbach da maki uku, Celtic da maki daya.
Haka kuma a ranar ta Talata Borussia Monchengladbach za ta karbi bakuncin Celtic a Jamus.