Schweinsteiger ya fara atisaye a Man United

Asalin hoton, Getty Images
Mourinho ne ya jagoranci atisayen da United ta yi a ranar Litinin
Dan kwallon tawagar Jamus, Bastian Schweinsteiger, ya fara yin atisaye da manyan 'yan wasan Manchester United.
Tun lokacin da Mourinho ya zama kociyan United, Schweinsteiger ke yin atisaye shi kadai ko kuma tare da matasan kungiyar 'yan kasa da shekara 23.
Rabon da Schweinsteiger tsohon kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Jamus ya buga wa United wasa tun a watan Maris karkashin Louis van Gaal.
Schweinsteiger ya yi wa United wasanni 31, tun lokacin da ya koma Old Trafford da murza-leda daga Bayern Munich kan kudi sama da fam miliyan 14 a Yulin 2015.