Kocin Jamus Low ya tsawaita yarjejeniyarsa

Kociyan tawagar kwallon kafa ta Jamus Joachim Low

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Jamus ce ke mataki na daya a kan teburin rukuni na uku a wasannin shiga gasar cin kofin duniya

Kociyan tawagar kwallon kafa ta Jamus, Joachim Low, ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da jan ragamar kasar har zuwa karshen gasar kofin nahiyar Turai ta 2020.

Kwantiragin Low, mai shekara 56, da Jamus za ta kare ne, bayan kammala gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Low ya dade yana jan ragamar tawagar Jamus, wanda ya yi wa Jurgen Klismann mataimaki na shekara biyu, kafin ya karbi aikin horar da kasar.

Kociyan ya lashe kofin duniya da aka yi a Brazil a shekarar 2014, a kuma shekara biyar ya kai kasar wasannin daf da karshe.

A gasar cin kofin ahiyar Turai da aka yi a shekarar 2016, mai masaukin baki Faransa ce ta fitar da Jamus a wasan kusa da na karshe a gasar.