Kociyan tawagar mata ta Nigeria na bin albashi

World Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Florence Omagbemi a lokacin da ta buga wa Nigeria kofin duniya a shekarar 2003

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF, ba ta biya mai horar da tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria, Florence Omagbemi, albashinta ba.

Omagbemi wadda ta wakilci Nigeria a gasar cin kofin duniya har sau hudu, ta yi watanni takwas tana aiki ba tare da an biya ta albashinta ba.

Sai dai kuma hukumar kwallon kafa ta Nigeria ta ce za warware matsalar kafin tawagar ta je Kamaru domin kare martabarta

Super Falcons wadda ke rike da kofin nahiyar Afirka, za ta kare kambunta a ranar 19 ga watan Nuwamba zuwa 3 ga watan Disamba a Kamaru.

Nigeria tana rukuni na biyu da ya kunshi Mali da Ghana da kuma Kenya.

Cikin masu horar da tawagar kwallon kafa ta Nigeria da suka bi hukumar albashi sun hada da Samson Siasia da Sunday Oliseh da marigayi Stephen Keshi.