Fifa ta kirkiro kyautar karrama 'yan kwallo

A ranar 9 ga watan Janairun 2017 Fifa za ta bayyana sunayen wadanda za ta karrama
Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta kirkiro sabuwar kyautar karrama 'yan wasan kwallon kafa da suka yi fice, bayan da ta raba gari da masu shirya kyautar Ballon d'Or.
Hukumar za ta sanar da wadanda za su lashe kyautuka takwas da ta ware tsakanin maza da mata masu taka leda da wadanda suke bayar da gudunmawa a fagen tamaula a ranar 9 ga watan Janairu a Zurich.
Fifa ta fara karrama 'yan wasa da jami'ai da suka taka rawar gani a fagen tamaula a shekarar 1991 zuwa 2009 daga nan ne ta hada gwiwa da mujallar Faransa mai gudanar da kyautar Ballon d'Or.
A karkashin wannan sabon tsarin za a fitar da zakarun bana ta hanyoyi biyu.
Hanyar farko kashi 50 cikin 100 zai kunshi kuri'un kyaftin da kociyoyin tawagar kwallon kafa da suke mambobi a hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa.
Haka kuma za a bai wa jama'a damar yin zabe ta intanet da kuma manyan 'yan jarida 200 da suke fadin duniyar nan.
A ranar Juma'a Fifa za ta bayyana 'yan wasa 23 da suke kan gaba a murza-leda, sannan ta ware guda uku a ranar 2 ga watan Disamba, wadanda daga cikinsu za a zabi zakaran bana.
Ga jerin kyautukan da za a lashe a shekarar 2016:
- Dan wasan da ya fi yin fice
- 'Yar wasan da ta fi yin fice
- Mai horarwa da ya fi kowa iyawa
- Wadda ta fi iya jan ragamar kwallon kafa ta mata
- Kwallon da aka ci mafi kayatarwa
- Kyautar wasa ba da gaba ba
- Kyautar magoya baya da suka fi da'a
- 'Yan wasa 11 da babu kamarsu a cikin fili