Za a fara damben mota na Matasa a Minna

Damben gargajiya
Bayanan hoto,

Shu'aibu ya ce ya shirya wasannin ne domin a haskaka matasan 'yan dambe a duniya

An tsara fara wasan damben gargajiya na matasan 'yan wasa a Minna da ke jihar Niger a ranar Talata.

Tun farko an tsara fara gasar a ranar Litinin, amma ruwan sama da ya sauka a ranar ya sa aka dage wasannin.

Shugaban kungiyar dambe ta Niger, Shu'aibu Ado Soja, ya ce sun dauki matakan da suka da ce domin a yi wasannin lafiya.

Ya kuma ce sun shirya gasar ce domin raya al'adun gargajiya, da kuma fito da matasan 'yan dambe da suke yi wasannin.

A gasar da za a gudanar babu manyan 'yan wasa da suka hada da Ebola da Mai Takwasara da Ali Kanin Bello.

Za a yi kwanaki 10 ana gudanar da wasannin, kuma zakara zai lashe motar hawa, na biyu ya karbi babur, sannan a bai wa na uku kudi.

Ga wasanni shida da za a yi a rana ta farko:

  • Autan Chika (Guramada ) da shagon Bata Isarka (Kudu)
  • Shagon Karamutsa (Jamus) da Bahagon Dogon Auta (Kudu)
  • Shagon Horon Kyande (Guramada) da Autan Fafa (Jamus)
  • Dan Kirisfo (Jamus) da Shagon Dogon Auta (Kudu)
  • Horon kyande (Guramada) da Shagon Shukurana (Jamus)
  • Shagon Dogon Jamilu (Jamus) da Shagon Dogon Kyallu (Guramada)