Inter Milan ta kori kociyanta de Boer

Serie A

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Frank de Boer ya buga wa Netherlands wasanni 112 ya kuma yi wa Ajax da Barcelona da Galatasaray da kuma Rangers

Inter Milan ta sallami kociyanta Frank de Boer, bayan da ya jagoranci kungiyar kwanaki 85.

De Boer ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku a Inter a watan Agusta, bayan da ya maye gurbin tsohon kociyan Manchester City, Roberto Mancini.

Inter tana mataki na 12 a kan teburin gasar Seria A ta Italiya, inda ta yi rashin nasara a hannun Sampdoria da ci 1-0 a ranar Lahadi, kuma wasa na hudu da aka doke ta daga guda biyar da ta yi.

Kungiyar ta nada mai horar da matasan 'yan kwallonta, Stefano Vecchi a matsayin kociyan rikon kwarya.

Kungiyar mai buga gasar Italiya na neman mai horar da 'yan wasa karo na tara tun bayan da Mourinho ya bar Inter a shekarar 2010.

Wadan da suka horar da Inter a cikin shekara shida sun hada da kociyan Newcastle United, Rafael Benitez da Claudio Ranieri na Leicester City da kuma mai jan ragamar Watford Walter Mazzarri.