FA ta sake tukumar Mourinho

Asalin hoton, Getty Images
United tana mataki na takwas a kan teburin Premier
Hukumar kwallon kafa ta Ingila, ta tuhumi kociyan Manchester United, Jose Mourinho, a karo na biyu a cikin mako daya.
Tun farko hukumar ta tuhumi Mourinho kan kalaman da ya yi kan alkalin wasa Anthony Taylor, wanda ya shugabanci karawar da United ta ziyarci Liverpool a gasar Premier.
Yanzu kuma ta sake tuhumar kociyan da laifin fadin kalaman batanci ga alkalan wasan da Man United ta tashi babu ci da Burnley a gasar Premier.
An bai wa Mourinho zuwa ranar Juma'a domin ya kare kansa, kuma watakila hukumar ta dauki matakin jan kunne ko cin tara ko dakatar da shi halartar wasan kungiyarsa zuwa wani lokaci.
United tana mataki na takwas a kan teburin Premier, kuma ta kasa cin wasa a cikin fafatawa hudu da ta yi.