Klose ya yi ritaya daga buga tamaula

Wold Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Klose ya lashe kofin duniya a shekarar 2014 da aka yi a Brazil

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Jamus, Miroslav Klose, ya yi ritaya daga murza-leda.

Tsohon dan kwallon Bayern Munich, ya taimaka wa Jamus lashe gasar cin kofin duniya a 2014.

Kuma ya karbi kyautar wanda ya fi cin kwallaye a tarihin gasar gaba daya, bayan da ya zura kwallo 16 jumulla a wasannin da ya halarta na lokaci daban-daban.

Klose wanda ya ci kofuna biyu na gasar Bundesliga a Bayern Munich, ya zauna ba shi da kungiyar da yake buga tamaula, bayan da yarjejeniyarsa ta kare da Lazio a karshen kakar bara.

Dan wasan wanda aka haifa a Poland ya yi wa Jamus wasanni 137, inda ya shafe tarihin yawan cin kwallaye da Gerd Muller ya kafa tsawon shekara 40 da cin kwallaye 68 a Yunin 2014.

Klose ya yi ritaya daga buga wa Jamus tamaula bayan da aka kammala gasar cin kofin duniya a Brazil a shekarar 2014, ya kuma ci wa tawagar kwallaye 71.

Yanzu haka yana shirin komawa cikin kociyoyin tawagar kwallon kafa ta Jamus, bayan da Joachim Low ya mika masa goron gayyata.