Joshua zai kare kambinsa na damben boksin

Boxing

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Joshua ya taba kare kambinsa na IBF a karon farko a cikin watan Yuni

Zakaran damben boksin ajin babban nauyi na IBF, Anthony Joshua, zai kare kambinsa a gumurzun da zai yi da Eric Molina a Manchester ranar 10 ga watan Disamba.

Joshua wanda bai je kasa ba a karawa 17, yana daf da kulla yarjejniyar karawa da Wladimir Klitschko, kafin maganar ta watse.

Mai kula da harkokin tsara dambe, Eddie Hearn, ya dora alhakin wargajewar yarjejeniyar karawar tsakanin 'yan damben biyu, bayan da aka ki saka kambun WBA da Tyson Fury ya ajiye a cikin wadanda za a ci.

Molina dan Amurka ya rasa kambinsa na WBC a hannun Deantay Wilder a shekarar 2015.

Joshua ya taba kare kambinsa na IBF a karon farko, bayan da ya yi wa Dominic Breazeale bugun kwaf daya a turmi na bakwai da suka kara a Landan a watan Yuni.