Wanda ya sassaka kofin duniya na kwallon kafa ya mutu

World Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Silvio Gazzaniga, ya mutu yana da shekara 95 a Milan ta Italiya

Mutumin da ya tsara ya kuma sassaka kofin duniya na gasar kwallon kafa, Silvio Gazzaniga, ya mutu yana da shekara 95 a Milan ta Italiya.

Gazzaniga wanda ake yi masa lakabi da Mai kofuna shi ne ya zana kofin Zakarun Turai da na Europa.

Shi ne kuma wanda ya kera kofi mai nauyin kilo shida da aka bai wa Brazil na din-din-din wanda ake kira Jules Rimet, bayan da ta ci kofin duniya na uku a shekarar 1970.

Mutane 53 ne suka yi takarar neman aikin zanawa da sassaka wa hukumar kwallon kafa ta duniya kofin duniya a shekarar 1971, inda ta zabi aikin Gazzaniga, wanda ya zana mutane biyu dauke da duniya a kafadarsu.