Manchester City ta ci Barcelona 3-1

Champions League

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

City za ta iya kaiwa wasan zagayen gaba idan ta ci Borrussia Monchengladbach a ranar 23 ga watan Nuwamba

Manchester City ta doke Barcelona da ci 3-1 a gasar cin kofin zakarun Turai da suka kara a ranar Talata a Ettihad.

Barcelona ce ta fara cin kwallo ta hannun Lionel Messi minti na 21 da fara wasa.

Sauran minti shida a je hutu ne City ta farke ta hannun Ilkay Gundogan, Kevin de Bruyne ya ci ta biyu bayan da aka dawo daga hutu, sannan Ilkay Gundogan ya ci ta uku kuma ta biyu da ya ci a karawar.

Da wannan sakamakon, Barcelona ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin rukuni na uku da maki tara, yayin da City ke matsayi na biyu da maki bakwai.

Borussia Monchengladbach wadda ta tashi kunnen doki 1-1 da Celtic a wasa na biyu na cikin rukuni, tana mataki na uku da maki hudu sai Celtic mai maki biyu.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

  • Besiktas 1 vs Napoli 1
  • Basel 1 vs Paris St G 2
  • Ludogorez 2 vs Arsenal 3
  • Benfica 1 Dynamo Kiev 0
  • Atl Madrid 2 vs FC Rostov 1
  • PSV Eindhoven 1 vs Bayern Munich 2