Horon Kyande ya buge Shukurana a damben mota

Damben gargajiya
Bayanan hoto,

Tun a ranar Talata aka fara gasar damben gargajiya ta mota a Minna, jihar Niger Nigeria

Horon Kyande Guramada ya kai wasan zagayen gaba a gasar damben gargajiya ta matasa da za a ci mota.

Horon Kyanden ya samu nasarar doke Shagon Shukurana daga Arewa ne a turmin na uku, a fafatawar da suka yi a ranar Laraba a Minna ta jihar Nijar Nigeria.

Shi ma Shagon Dogon Dan Jamilu daga Arewa ya kai zagayen gaba, bayan da ya samu nasara a kan Shagon Sojan Kyallu Guramada a turmin farko.

Shi kuwa Shagon Kato Mai Karfi daga Kudu buge Autan Makada Guramada ya yi a turmi na biyu,

Shagon Dogon Dan Digiri daga Kudu kuwa ya kai zagaye na biyu ne a gasar bayan da abokin karawarsa Bahagon Audu Argungu bai halarci filin ba.

Tun a ranar Talata aka fara gudanar da gasar a filin wasa na U.K Bello Art and Theater da ke Minna a jihar Niger, kuma kwanaki goma za a gudanar da wasannin.