An bayyana alkalan gasar cin kofin Afirka ta Mata

Kamaru

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kamaru ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta kwallon kafar mata

An bayyana sunayen alkalan wasa 25 da za su jagoranci gasar cin kofin nahiyar Afirka ta kwallon kafar mata da za a yi a watan Nuwamba.

Cikin sunayen da hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf, ta fitar guda 11 ne za su yi hura a wasannin, yayin da 14 za su taimaka musu wajen gabatar da aikin.

Za a fara gasar ne a ranar 19 ga watan Nuwamba zuwa 3 ga watan Disambar 2016 a birnin Yaounde da Limbe a Kamaru.

Rukunin farko ya kunshi mai masaukin baki Kamaru da Afirka ta Kudu da Zimbabwe da Masar.

Rukuni na biyu ya hada da mai rike da kofin, Nigeria da Ghana da Kenya da kuma Mali.

Ga jerin alkalan wasan da za su jagoranci wasannin:

Alkalan wasa

  • Maria Packuita Cynquela Rivet Mauritius
  • Salma Mukansanga Rwanda
  • Gladys Lengwe Zambia
  • Lidya Tafesse Habasha
  • Akhona Zennith Makalima Afirka ta Kudu
  • Jeanne Ekoumou Kamaru
  • Aissata Ameyo Amegee Togo
  • Suavis Iratunga Burundi
  • Caralyne Wanjala Kenya
  • Jonesia Rukyaa Kabakama Tanzaniya

Mai jiran Kar-ta-kwana

11. Letticia Antonella Viana