Fifa ta fitar da 'yan takarar koci da ya fi yin fice

Fifa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A cikin watan Janairun 2017 za a bayyana kociyan da ya fi yin fice a bana

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta fitar da jerin sunayen masu horar da kwallon kafa guda 10 da za a zabi wanda ya fi yin fice a bana.

Cikin wadanda hukumar ta bayyana sun hada da Didier Deschamps (france) da Luis Enrique (spain) da Fernando Santos (portugal) da Diego Simeone (Argentina) da kuma Zenedine Zidane (Real Madrid).

Sauran sun hada da Chris Coleman (Wales) da Claudio Ranieri (Leicester City) da Pep Guardiola (Manchester City) da Jurgen Klopp (Liverpool) da kuma Mauricio Pochettino (Tottenham Hotspur).

A ranar 9 ga watan Janairu ne hukumar kwallon kafar ta duniya, Fifa, za ta sanar da gwarzon mai horar da tamaulan da ya fi yin fice a duniya.

Hukumar za ta gudanar da zaben ne ta hanya biyu, a karkashin sabon tsari, bayan da ta raba gari da mujallar Faransa mai bayar da kyautar Ballon d'Or.

Hanyar farko, ita ce, kashi 50 cikin 100 zai kunshi kuri'un kyaftin-kyaftin da kociyoyin tawagar kwallon kafa da suke mambobi a hukumar kwallon kafar ta duniya.

Haka kuma za a bai wa jama'a damar yin zabe ta intanet da kuma manyan 'yan jarida 200 da suke fadin duniyar nan.