FA ta hukunta Jose Mourinho

Premier

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

A cikin mako daya hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi Mourinho da laifuka biyu

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta hukunta kociyan Manchester United, Jose Mourinho, inda ta ce ba zai ja ragamar kungiyar ba a wasa daya.

Hukumar ta yanke wannan hukuncin ne, bayan da alkalin wasa Mark Clattenburg ya bai wa kociyan jan kati a karawar da United ta tashi wasa babu ci da Burnley a gasar Premier.

Hukumar ta kuma ci kociyan tarar kudi fam 8,000, haka kuma wasan da United za ta yi da Swansea ne hukuncin zai yi aiki a kansa.

Haka kuma hukumar ta ci tarar Mourinho kudi fam 50,000 kan batun da ya yi a kan nada alkalin wasa Anthony Taylor.

Mourinho ya ce nada Taylor a matsayin wanda ya hura karawar da suka yi da Liverpool a Anfield an sa shi cikin matsi.

A bisa doka ba a yadda mai horar da kwallon kafa ya yi jawabi kan alkalin tamaula kafin a buga wasa ba.