Ana zargin Sanchez da kin biyan haraji

Arsenal

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sanchez ya buga wa Arsenal wasan gasar zakarun Turai a ranar Talata

Masu shigar da kara a Spaniya na zargin Alexis Sanchez da kin biyan haraji a lokacin da yake kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.

Masu shigar da karar sun ce Sanchez mai shekara 27, bai biya harajin kudin da ya kai fam £888,246 daga tsakanin shekarar 2012 da 2013.

Sun kuma ce dan kwallon ya yi amfani ne da wani kamfani a Malta domin yin rufa-rufar harajin da za a caje shi kan kudaden talla da yake samu a fagen tamaula.

Sanchez ya koma Arsenal da Murza-leda daga Barcelona kan kudi fam miliyan 35 a shekarar 2014.