Legia da Real Madrid sun tashi wasa 3-3

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Legia ta karbi bakuncin Real Madrid a filin wasanta ba tare da 'yan kallo ba

Legia Warsaw da Real Madrid sun tashi wasa 3-3 a gasar cin Kofin Zakarun Turai da suka fafata a ranar Laraba.

Gareth Bale ne ya fara ci wa Madrid kwallo a mintin farko da fara wasa, kuma Kareem Benzema ya kara ta biyu saura minti 10 a je hutun rabin lokaci.

Saura minti biyar a je hutu ne, Legia ta zare kwallon farko ta hannun Odjidja-Ofoe da kuma ta biyu ta hannun Radovic, sannan ta ci ta uku saura minti bakwai a tashi daga karawar ta hannun Moulin.

Sai dai kuma ya rage saura minti biyar alkalin wasa ya tashi fafatawar Madrid ta farke ta hannun Kovacic.

Da wannan sakamakon Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin rukuni na shida, yayain da Legia ce ta karshe da maki daya.

Borussia Dortmund wanda ta ci Sporting 1-0 a ranar ta Laraba ce ke matsayi na daya da maki 10, ita kuwa Sporting tana da maki uku a mataki na uku.

Ga sauran sakamakon wasannin da aka yi:

  • Monaco 3 vs CSKA 0
  • Tottenham 0 vs Bayer Levkn 1
  • Bor Dortmd 1 vs Sporting 0
  • FC Copenhagen 0 vs Leicesterm 0
  • FC Porto 1 vs Club Brugge 0
  • Juventus 1 vs Lyon 1
  • Sevilla 4 vs Dinamo Zagreb 0