Golan Leicester City ya tafi doguwar jiyya

Asalin hoton, Rex Features
A watan Agusta Schmeichel ya kulla yarjejeniyar shekara biyar da Zakarun Premier, Leicester
Golan kungiyar Leicester Kasper Schmeichel zai jima bai dawo filin wasa ba sakamakon raunin da ya ji a hannunsa a karawar da suka yi da kungiyar FC Copenhagen a gasar cin kofin Zakarun Turai ranar Laraba.
Schmeichel, mai sheakara 29 ya ji raunin ne a hannunsa na dama tun kafin a tafi hutun rabin lokaci amma ya jure har aka tashi wasan canjaras ba ci.
Kungiyar Leicester ta kafa tarihi a gasar ta Zakarun Turai, na kasancewa wadda ta yi wasanni hudu na farko ba tare da an ci ta ba.
Hukumar kungiyar ta Leicester ta ce dan wasan dan kasar Denmark zai dauki tsawon lokaci kafin ya dawo wasa.
Mai tsaron ragar ya kama wa kungiyar a dukkanin wasanninta na gasar Premier 38 a kakar da ta gabata da suka dauki kofi, inda ba a zura masa kwallo a raga ba a wasanni 15.
Ya yi wa kulob din sama da wasanni 200 tun lokacin da ya koma Leicester din daga Leeds United a 2011, tun bayan da ya fara wasansa a Manchester City.
Ron-Robert Zieler wanda dan tawagar kasar Jamus ce da ta ci kofin duniya na 2014, mai shekara 27 shi ne zai rika kama wa kungiyar kafin Schmeichel ya warke.
Wasan da Zieler ya kama wa Leicester na karshe shi ne wanda Manchester United ta ci su 4-1 ranar 24 ga watan Satumba.
Golan zai shiga raga ne a wasan Premier da Leicester din za ta yi a gida da West Brom ranar Lahadi.