Wenger ya soki Fifa a kan Ingila da Scotland

Arsene Wenger
Bayanan hoto,

Wenger ya ce bai dace Fifa ta hana Ingila da Scotland al'adar mutunta wadanda suka mutu don kasarsu ba

Kocin Arsenal, Arsene Wenger, ya ce Fifa, ba ta yi daidai ba da ta hana 'yan wasa sanya kyallaye masu alamar tunawa da sojin Burtaniya da na Commonwealth da suka mutu a yakin duniya na daya da sauran rikice-rikice, a wasan neman shiga gasar kofin duniya da Ingila za ta yi da Scotland.

Kocin na Arsenal ya ce, bai kamata Fifa ta shiga wannan lamari ba, yana mai karin bayani da cewa, wani lokaci idan kana son ka nuna cewa daidai kake a kan akidarka ta siyasa, sai ka dan saba wa al'ada.

Kocin ya ce, ''ina ganin wannan na daga al'adar Ingila da nake kauna. Suna mutunta al'ada, kuma suna martaba mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu ga kasar.''

Ita dai hukumar ta haramta sanya sakonnin siyasa ko addini ko wata talla a jikin rigunan 'yan wasa.

alamar tunawa da sojin Burtaniya da na kwamanwelz
Bayanan hoto,

Wani dan wasan Ingila sanye da alamar da ake ce-ce-ku-ce a kanta, ta tunawa da sojin Burtaniya da na kungiyar Commonwealth

Ita dai wannan alama ana sanya ta ne a makonnin kusa da kuma ranar 11 ga watan Nuwamba, domin tunawa da sojin na Burtaniya da na kungiyar kasashen renon Ingila da suka mutu a yakin duniyar na daya da sauran yake-yake da suka biyo baya.

Babbar Sakatariyar Fifa, Fatma Samba Diouf Samoura za ta gana da ranar Alhamis din nan da hukumomin kwallon kafa da ke Burtaniya a filin wasa na Wembley, kuma mai yuwuwa su tattauna a bayan fage kan batun in ji wakilin BBC.

Samoura ta sheda wa BBC cewa, kowane irin hukunci zai iya biyo baya, idan aka saba wannan umarni na hukumar ta kwallon kafa ta duniya.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila, Martin Glenn, ya gaya wa BBC cewa, 'yan wasan bangarorin biyu za su yi watsi da wanna umarni na Fifa, su sanya wannan jar alama, a matsayin al'adarsu.

Ita ma hukumar kwallon kafa ta Scotland ta ce a shirye take ta kalubalanci duk wani hukunci da Fifa za ta yi wa 'yan wasanta kan daura kyalle a hannuwansu, wato wannan alama.

A ranar Juma'a ta sama ne 11 ga watan Nuwamba kungiyoyin na Ingila da Scotland za su kara a wasan neman tikitin zuwa gasar cin kofin duniya na 2018, a filin wasa na Wembley.

Fifa dai ta bar 'yan wasan Ingila da na Scotland din sun sanya wannan alama da yanzu ake wannan ja-in-ja a kanta, a kan bakin kyalle, suka daura a hannuwansu, a lokacin wasan kasa da kasa a watan Nuwamba na 2011.