Jason Brown na damuwa bayan ritaya

Jason Brown

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto,

Jason Brown ya ce rayuwa bayan ritaya daga kwallon kafa na cike da damuwa

Kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa ta Ingila (PFA), ta ce rayuwar 'yan wasan da suka yi ritaya daga buga tamola daidai take da ta tsofaffin sojoji , saboda yadda suke fafutuka da rayuwa a karshen sana'ar tasu.

Kungiyar ta ce an samu karuwar kashi 25 cikin dari na yawan 'yan wasan da suke neman taimako kan matsalolin tabin hankali da damuwa a shekarar da ta wuce.

Tsohon mai tsaron ragar Wales da kuma kungiyar Gillingham da Aberdeen Jason Brown ya sheda wa BBC yadda ya iya rayuwa da raunin da aka ji masa a fuska da kuma kunnensa a lokacin wasansa.

Amma yana ganin abu mafi wuya a wurinsa shi ne, tunanin abubuwan da ya yi ba daidai ba da kuma kudin da zai rika kashewa idan ya yi ritaya.

Tsohon golan ya ce, ''ba na barci, ba na cin abinci. Tun ina dan shekara takwas ba abin da nake yi sai kwallon kafa.

Sai kuma kawai wannan abu da nake yi, wato wasan kwallon kafar ya bace ( ya zo karshe). To yanzu na fahimci dalilin da ya sa mutane ke kashe kansu.''