Kofin Europa: Fernebahce ta doke Man United 2-1

Moussa Sow

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Kwallon farko da Moussa Sow ya sheka wa Man United kenan

Fernebahce ta doke Manchester United 2-1 a karawar da suka yi ta biyu ta kofin Zakarun Turai na Europa wasan mako na hudu na rukunin farko.

Kungiyar ta birnin Istanbul ta fara daga ragar bakin nata ne a cikin minti biyu kacal da shiga fili ta hannun dan wasanta Sow, wanda ya shammaci 'yan Unitd din ya yi kwance-kwance da baya ya sheka musu ita a raga.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma a minti na 59 J. Lens ya kara kwallo ta biyu a ragar Manchester United.

Wayne Rooney ya rama wa Man United din kwallo daya ana dab da tashi daga wasan a minti na 89.

Kwallon ta Rooney ita ce ta 38 da ya ci a gasar Zakarun Turai, wadda ta sa ya kamo Ruud van Nistelrooy a matsayin wanda ya fi ci wa United kwallo a gasar Zakarun Turai.

Sakamakon ya sa United ta zama ta uku a rukunin na farko (Group A), da maki daya a bayan Feyenoord da Fenerbahce.

Kuma hakan ya jefa ta cikin hadarin kasa zuwa mataki na gaba na sili-daya-kwale, na gasar ta kofin Europa.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wasa biyu ya rage wa kungiyar ta Premier, inda za ta kara a Old Trafford da Feyenoord ta Holland, sannan kuma ta je Ukraine ta hadu da Zorya Luhansk.

A karawarsu ta farko mako biyu da ya gabata Manchester United ta ci Fernebahce 4-1 a Old Trafford.

A daya karawar da ka yi ta rukunin na daya Zorya Luhansk da Feyenoord sun yi canjaras 1-1.

Ga sakamakon wasu daga cikin wasannin na ranar Alhamis gguda 24:

Astana 1 - 1 Olympiakos Piraeus

Athletic Club 5 - 3 Genk

Sassuolo 2 - 2 Rapid Wien

Austria Wien 2 - 4 Roma

Astra 1 - 1 Viktoria Plzeň

Zenit 2 - 1 Dundalk

Maccabi Tel Aviv 0 - 0 AZ

APOEL 1 - 0 Young Boys

Fenerbahçe 2 - 1 Manchester United

Zorya 1 - 1 Feyenoord

Qabala 1 - 2 Saint-Étienne

Anderlecht 6 - 1 Mainz 05

Ajax 3 - 2 Celta de Vigo

Panathinaikos 0 - 3 Standard Liège

Zürich 0 - 0 Steaua Bucureşti

Villarreal 1 - 2 Osmanlıspor

Sparta Praha 2 - 0 Hapoel Be'er Sheva

Southampton 2 - 1 Internazionale

Gent 3 - 5 Shakhtar Donetsk

Sporting Braga 3 - 1 Konyaspor

Fiorentina 3 - 0 Slovan Liberec

PAOK 0 - 1 Qarabağ

Schalke 04 2 - 0 Krasnodar

Nice 0 - 2 Salzburg