Sunan kofin League Cup na Ingila zai koma Carabao

Manchester City, Capital Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City ce ta dauki kofin a bara lokacin ana kiransa Capital One

Kofin League Cup na kawllon kafa na Ingila (EFL), zai samu sabon suna daga kaka mai zuwa ta 2017-18, inda za a rika kiransa kofin Carabao, a karkashin wata yarjejeniya da aka kulla ta daukar nauyin gasar.

Hukumar gasar cin kofin ta kulla yarjejeniyar tsawon shekara uku a kan fam miliyan 18 da kamfanin lemon gwangwani na kara kuzari na kasar Thailand.

Yarjejeniyar ta dan zarta wadda masu gasar kofin suka taba yi a baya da kamfanin samar da katin karbar kudi na banki, na Amurka mai suna Capital One.

Kamfani Carabao, na kasar ta Thailand daman tuni ya kulla yarjejeniyar daukar nauyin kungiyar Reading.

Kamfanonin da suka taba kulla irin wannan yarjejeniya ta daukar gasar cin kofin sun hada da Milk Marketing Board da Littlewoods da Rumbelows da Coca-Cola da Worthington's da kuma Carling.