Andy Murray ya dare mataki na daya a Tennis

Asalin hoton, AFP
Murray dan Birtaniya na farko da ya dare matsayi na daya a iya kwallon tennis a duniya
Andy Murray zai hau mataki na daya a karon farko a jerin wadanda suke kan gaba a gasar kwallon tennis a duniya.
Murray ya samu wannan damar ce, bayan da Milos Raonic ya ce ba zai iya buga wasan daf da karshe ba da shi a ranar Asabar a gasar kwararru a Paris, sakamakon raunin da ya yi.
Tun farko Murray na bukatar kai wa wasan karshe a gasar ta Paris, bayan da wanda ke matsayi na daya Novak Djokovic ya kasa kai bantensa a ranar Juma'a.
Tun kafin ranar Asabar Raonic ya ce ba zai iya buga wasan daf da karshe ba a ranar Asabar saboda raunin da ya yi, hakan ne ya sa Murray ya kai wasan karshe a gasar.
Murray zai zama dan wasan tennis na farko dan Birtaniya da ya taka wannan matsayin tun lokacin da hukumar tennis ta fara fitar da jadawalin wadanda suke kan gaba a wasan a 1973.
A kakar bana Murray ya kai wasannin karshe sau 11 a karawa 12, inda ya ci wasanni 73 a kakar kwallon tennis ta bana.
A ranar Litinin za a bayyana shi a mataki na daya, a lokacin da hukumar za ta fitar da jadawalin wadanda suke kan gaba a iya wasan a duniya,