Man City da Middlesbrough sun tashi wasa 1-1

Premier

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Kwallo na 14 da Aguero ya ci daga wasanni 15 da ya buga a kakar bana

Manchester City da Middlesbrough sun raba maki daya da daya a tsakaninsu, bayan da suka tashi wasan Premier 1-1 a gasar mako na 11 da suka kara a Ettihad.

City ce ta fara cin kwallo ta hannu Sergio Aguero kuma ta 150 da ya ci wa kungiyar tun lokacin da ya koma can da taka-leda.

Daf da za a tashi daga fafatawar Boro ta farke ta hannun De Roon.

Da wannan sakamakon City ta hada maki 24, yayin da Boro ke da maki 11.

City za ta ziyarci Crystal Palace a wasan mako na 12, ita kuwa Boro za ta karbi bakuncin Chelsea ne.