Chelsea ta dare kan teburin Premier

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Eden Hazard ne ya ci kwallaye biyu a Stamford Bridge

Chelsea ta shararawa Everton kwallaye 5-0 a gasar Premier wasan mako na 11 da suka fafata a Stamford Bridge.

Eden Hazard ne ya fara cin kwallo, sannan Marcos Alonso ya ci biyu, kuma daf da za a je hutun rabin lokaci Diego Costa ya kara ta uku.

Bayan da aka dawo daga hutu ne, Eden Hazard ya kara ta hudu kuma ta biyu da ya ci a karawar, daga karshe Pedro ya ci ta biyar.

Da wanana sakamakon Chelsea wadda ta yi wasanni 11 ta koma mataki na daya a kan teburin Premier da maki 25.

Chelsea za ta buga wasan gaba ne da Middlesbrough, yayin da Everton za ta karbi bakuncin Swansea City a wasannin mako na 12 a gasar ta Premier.