Kano Pillars ta nada Ikhana sabon kociyanta

Kano Pillars

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Wannan ne karo na hudu da Ikhana zai horar da Kano Pillars

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta nada Khadiri Ikhana a matsayin wanda zai horar da 'yan wasanta.

Kano Pillars da Ikhana sun kulla yarjejeniyar yin aiki ta shekara daya, daga baya su sake tattaunawa idan tafiyar ta yi kyau.

Ikhana zai maye gurbin Baba Ganaru wanda ya yi murabus bayan kammala gasar Firimiyar bana, yanzu ya koma horar da Wikki Tourists ta Bauchi.

Wannan ne karo na hudu da Ikhana zai ja ragamar Pillars, bayan da ya yi a 1991 da 1997/98 da 2007/08,

Ikhana tsohon kociyan Enyimba ya koma aiki da Pillars daga Shooting Stars.