Arsenal da Tottenham sun tashi wasa 1-1

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rabon da Kane ya buga wa Tottenham tamaula tun a ranar 18 ga watan Satumba

Arsenal da Tottenham sun tashi wasa kunnen doki 1-1 a gasar Premier wasan mako na 11 da suka fafata a Emirates a ranar Lahadi.

Arsenal ce ta fara cin kwallo, bayan da Mesut Ozil ya yi bugun tazara Kevin Wimmer ya ci gida wato Tottenham.

Tottenham ta farke ta hannun Harry Kane a bugun fenariti, bayan da Koscielny ya yi wa Mousa Dembele keta a da'ira ta 18.

Da wannan sakamakon Arsenal ta koma mataki na uku, yayin da Tottenham ta koma matsayi na biyar a kan teburin na Premier bayan da suka yi wasanni 11 a gasar.