Real Madrid ta doke Leganes da ci 3-0

Asalin hoton, Getty Images
Bale ya ci wa Real Madrid kwallaye uku a wasanni biyu da ya buga mata a kwanan nan
Real Madrid ta ci gaba da zama a matsayi na daya a kan teburin La Liga, bayan da ta ci Leganes 3-0 a gasar Spaniya wasan mako na 11 da suka kara a ranar Lahadi.
Real ta fara cin kwallo ne ta hannun Gareth Bale, wanda ya sake saka hannu a kan yarjejeniyar ci gaba da murza leda a Madrid a ranar Lahadi da ta wuce.
Gareth Bale dan kwallon tawagar Wales, shi ne ya kara ta biyu a raga daf da za a je hutun rabin lokaci.
Alvaro Morata ne ya ci ta uku bayan da aka dawo daga hutun, wanda hakan ya sa Madrid ta hada maki uku rigis a fafatawar.
Madrid wadda ta hada maki 27 a wasanni 11 a gasar ta La Liga, ta ci gaba da zama a kan teburin a matsayi na daya.