Garkuwan Alabo ya buge Mahaukaci Teacher

Damben gargajiya
Bayanan hoto,

A turmin farko Garkuwan Shagon Alabo ya buge Shagon Mahaukaci Teacher

Garkuwan Shagon Alabo ya yi nasarar buge Shagon Mahaukaci Teacher a dambatawar da suka yi a gidan damben Ali Zuma a ranar Lahadi da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Garkuwan Shagon Alabo dan damben Kudu ya buge Shagon Mahaukacin Teacher ne daga Arewa a turmin farko da suka taka damben.

Tun farko Shagon Bahagon Falgore ne daga Kudu ya buge Shagon Autan Fafa daga Arewa a turmin farko.

Shi ma Shagon Shagon Mada daga Kudu buge Shagon Buzu daga Arewa ya yi, da farko Shagon Buzu bai amince da kisan farko ba, suka sake takawa dambe aka kara buge shi a karo na biyu.

Ga sauran wasannin da aka yi babu ci:

  • Shagon Shagon Dan Kanawa daga Kudu da Garkuwan Bagaon Balan Gada daga Arewa
  • Shagon Caka-Caka daga Arewa da Autan Faya daga Kudu
  • Dodon Dan Jamilu daga Arewa da Bahagon Sisco daga Kudu
  • Dogon Minsta daga Kudu da Autan Fafa daga Arewa
  • Autan Faya daga Kudu da Bahagon Abba daga Arewa.