Ronaldo zai sa hannu kan ci gaba da wasa a Real Madrid a ranar Litinin

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A ranar Litinin Cristiano zai amince da kulla sabuwar yarjejenia da Madrid

Cristiano Ronaldo ya amince zai saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da murza-leda a Real Madrid har zuwa kakar wasan 2021 a ranar Litinin.

Tun farko kwantiragin Ronaldo mai shekara 31, da Madrid za ta kare a watan Yunin 2018, idan ya tsawaita zamansa a kungiyar, za ta cika a lokacin da ya kai shekara 36.

Ana kuma rade-radin cewar dan wasan tawagar Portugal zai karbi albashin da zai kai fam 365,000 a kowanne mako.

Ronaldo ya ci kwallaye 371 tun lokacin da ya koma Madrid da taka-leda daga Manchester United a shekarar 2009.