Murray ya lashe gasar tennis ta Paris

Tennis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Murray ya taka rawar gani a kakar wasan shekarar 2016

Andy Murray ya dare mataki na daya a jerin wadan da suke kan gaba a wasan kwallon tennis a duniya, bayan da ya lashe gasar kwararru ta Paris a ranar Lahadi.

Murray dan Birtaniya ya samu nasarar doke John Isner 6-3 6-7 (4-7) 6-4, kuma nasarar lashe gasa ta shida da ya yi kenan a shekarar 2016.

Dan wasan mai shekara 29, ya lashe lambar yabo ta zinare a gasar Olympic a Brazil da gasar Wimbledon da suka taimaka masa kai wa matsayi na daya a wasan a duniya.

A ranar Litinin ake sa ran bayyana Murray a matsayin na daya a jerin wadanda suke kan gaba a iya kwallon tennis a duniya.

Shi ne dan wasan Birtaniya na farko da ya kai wannan matakin, tun lokacin da hukumar wasan kwallon tennis ta bullo da jadawalin 'yan wasan da suke kan gaba a tennis a duniya a shekarar 1973.